Kylian Mbappe da Vinicius Jr da kuma Erling Haaland su ne ’yan wasan kwallon kafa da suka fi tsada a duniya, a cewar wani bincike da cibiyar da ke nazari kan harkokin kwallon kafa ta CIES Football Observatory ta gudanar.
Mbappe, mai shekara 23, wanda ya ki amincewa ya tafi Real Madrid, inda ya ci gaba da zama a Paris St-German, shi ne kan gaba a cikin ’yan wasa mafiya tsada a duniya, wanda darajarsa ta kai Yuro miliyan 205.6 (Fam miliyan 175.7- kimanin Naira biliyan 136 da miliyan 343 da dubu 200 a kasuwar bayan fage).
Dan wasan Real Madrid dan kasar Brazil Vinicius Jr, wanda ya zura kwallon da ta ba su nasara a wasan karshe na gasar Zakarun Turai da suka fafata da Liverpool, shi ne na biyu mafi tsada wanda darajarsa ta kai Fam miliyan 158.3, yayin da dan kasar Norway da ke murza leda a Manchester City, Haaland ya zamo na uku inda ya kai Fam miliyan 130.4.
Dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund Jude Bellingham (Fam miliyan 114.1) shi ne dan kasar Ingila mafi tsada, wanda yake a matsayin na biyar a jadawalin, inda yake gaban takwaransa na Ingila kuma dan wasan Manchester City, Phil Foden da yake matsayin na shida da (Fam miliyan 105.9).
Kungiyoyin da suke fafatawa a Gasar Firimiya su ne suka mamaye jerin ’yan kwallon da suka fi tsada, inda ’yan wasa 41 suka fito a cikin ’yan kwallo 100 da suka fi daraja.
CIES ta yi amfani da wasu muhimman abubuwa da suka hada da shekarun dan wasa da kwazonsa da tattalin arzikin kungiyarsa da kuma hauhawar farashi wajen gudanar da wannan bincike.
Dan wasan Faransa Mbappe ya sa hannu a kan kwantaragin shekara uku a PSG a watan jiya yayin da ya zabi ci gaba da zama a Paris maimakon tafiya Real Madrid.
’Yan wasa 10 mafiya tsada a duniya kamar yadda CIES Football Observatory ta fitar su ne:
1. Kylian Mbappe – Paris St-Germain- Fam miliyan 175.7
2. Binicius Jr- Real Madrid – Fam miliyan 158.3
3. Erling Haaland – Borussia Dortmund – Fam miliyan 130.4
4. Pedri – Barcelona – Fam miliyan 115.4
5. Jude Bellingham – Borussia Dortmund – Fam miliyan 114.2
6. Phil Foden – Manchester City – Fam miliyan 105.9
7. Frenkie de Jong – Barcelona – Fam miliyan 96.1
8. Luis Diaz – Liverpool – Fam miliyan 94.0
9. Ruben Diaz – Manchester City – Fam miliyan 93.6
10. Ferran Torres – Barcelona – Fam miliyan 93.5.