A karshen watan jiya ne aka kammala cin kasuwar ’yan kwallon kafa a wasu kasashen Turai, inda kasuwarIngila ta fi hada-hada mai tsoka a cinikin ’yan wasan da ake yi a Turai.
Jaridar L’Ekuipe ta Faransa ta wallafa sunayen ’yan kwallo goma da suka fi daukar albashin mai tsoka a kowane wata a kasar kamar yadda BBC Hausa ya ruwaito kamara haka.
– Neymar (PSG) Fam miliyan 3.06 (Naira biliyan 1 da miliyan 358 da 640).
– Edinson Cabani (PSG) Fam miliyan 1.54 (Naira miliyan 683 da dubu 760).
– Kylian Mbappe (PSG) Fam miliyan 1.5 (Naira miliyan 666).
– Thiago Silba (PSG) Fam miliyan 1.33 (Naira miliyan 590 da dubu 520).
– Angel Di Maria (PSG) Fam miliyan 1.12 (Naira miliyan 497 da dubu 280).
– Markuinhos (PSG) Fam miliyan 1.12 (Naira miliyan 497 da dubu 280).
– Thiago Motta (PSG) Fam dubu 875, (Naira miliyan 388 da dubu 500).
– Jabier Pastore (PSG) Fam dubu 770, (Naira miliyan 341 da dubu 880).
– Radamel Falcao (Monaco) Fam dubu 750 (Naira miliyan 333).
– Dani Albes (PSG) Fam dubu 700, (Naira miliyan 310 da dubu 800).