✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwadago za su fara yajin aiki saboda dukan da aka yi wa shugabansu

Kungiyoyin sun ce muddin da a biya musu bukatunsu ba, za su fara yajin aikin

Gamayyar kungiyoyin kwadago na Najeriya na NLC da TUC sun ayyana tsunduma yajin aiki daga ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba don nuna bacin ransu da harin da aka kai wa shugabansu na kasa, Joe Ajaero, a Jihar Imo.

Aminiya ta rawaito yadda aka zargi jami’an ’yan sandan da suke aiki tare da Gwamnan Jihar da lakada wa Joe duka yayin wata zanga-zangar ’yan kwadago a Jihar, a makon da ya gabata.

Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja ranar Juma’a, Babban Sakataren TUC na kasa, Nuhu Toro, wanda ya sami rakiyar wasu shugabannin NLC, ya kuma ce sun bukaci a gaggauta canza wa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ahmed Barde, wajen aiki daga Jihar.

Ya ce, “’Yan sanda sun kumbura wa Kwamared Joe Ajaero idanu, sun masa dukan tsiya, sun tozarta shi, sun yaga masa rigar mutunci, sannan sun kai shi wajen da ba a sani ba, suka ci gaba da azabtar da shi, har aka yi masa barazanar kisa.

“Sai dai daga bisani ya sami dauki daga wajen mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

“Sai dai saboda tsananin dukan da ya sha, sai da ’yan sanda suka kai shi asbitinsu. Amma a lokacin da muka ziyarce shi a can, idonsa ya kumbura, ya yi ja, ba ma ya iya gane mutane.

“Duk jikinsa ya kukkumbura. Ba ma ya iya tafiya sai an taimaka masa. A sakamakon haka, tilas muka dauke shi muka kai Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Owerri don a ci gaba da duba lafiyarsa.

“… Saboda haka, muddin gwamnati ta gaza cika kowanne daga cikin sharudan da muka fi daya mata, NLC, TUC da rassansu ba za su ci gaba da aiki ba a kasar nan daga ranar Laraba mai zuwa, 8 ga watan Nuwamban 2023.

“Kazalika, kungiyoyin biyu za su gudanar da taron Gamayyar Majalisun Zartarwarsu, domin daukar mataki na gaba,” in ji Nuhu Toro.