✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan kungiyar asiri sun shiga hannun ’yan sanda

’Yan sanda sun kama ’yan kungiyar asiri guda 11 a lokacin da suke tsaka da bikin ratsuwar shiga kungiyar a Jihar Kuros Riba. Kakakin Rundunar…

’Yan sanda sun kama yan kungiyar asiri guda 11 a lokacin da suke tsaka da bikin ratsuwar shiga kungiyar a Jihar Kuros Riba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Irene Ugbo, “An same su da bindigogin katako da ganguna da jarkokin magunguna da kwalaben giya”, kuma sun hada da maza tara da mata shida.

Ya ce ’yan sanda masu yaki da fashi sun kama wadanda ake zargin ne bayan samun “kwararan bayanan sirri daga jama’a”.

Ugbo ya ce, “Daga nan a ranar 14 ga watan Agusta rundunar yaki da fashi da kwamishinan ’yan sanda ya kafa suka kai samame inda suka kama wadanda ake zargi da ayyukan kungiyar asiri.

“Wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu amma ana ci gaba da bincike domin gano sauran ’yan kungiyar.

“Kwamishinan ’yan sandan jihar yana gargadin duk ’yan kungiyar asiri da masu shirin shiga da su shiga taitayinsu”, inji jami’in.

Ugbo ya yi kira ga ’yan Jihar Kuros Riba da su ci gaba da harkokinsu ba tare da wata damuwa ba domin rundunar a tsaye take domin ta sa kafar wando da masu aikata laifuka.