✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan kungiyar asiri 60 sun shiga hannu a Binuwai

‘Yan sanda sun kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne guda 60 cikin sati daya a wurare daban-daban na garin Makurdi, Babban birnin…

‘Yan sanda sun kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne guda 60 cikin sati daya a wurare daban-daban na garin Makurdi, Babban birnin Jihar Binuwai.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, DSP Catherine Anene ta ce a kokarin rundunar na dakile matsalolin tsaro a fadin Jihar ne ta kai farmaki a kan kungiyoyin asiri bayan samun bayanan sirri da ke alakanta su da munanan laifuka a Jihar.

“A samamen da muka kai cikin sati daya, mun kama ‘yan kungiyar asiri 60 da bidigogi 4 da gatari 5 da hulunan beret bakake 3 da jajaye 2 sai kakin soja 1 da kuma rigar sulke 1”, inji.

Anene ta kara da cewa mutum takwas daga cikin wadanda ake zargi ‘yan kungiyar asiri ne an kama su ne a wani bangare cikin garin Makurdi, ranar 14 ga watan Yuni, 2020.

Ta ce bayan kwana daya sun kama wani da aka fi sani da “Smooky of North-Bank” tare da wasu mutum 17 kusa da North bank, sai kuma wani gungun mutum biyar a cikin garin, baya ga wasu kame da suka yi.

Jami’ar ta jaddada cewar rundunar a shirye take ta yaki miyagun laifuka kuma tana maraba da duk wanda zai ba ata bayanin da zai taimaka wajen kama masu laifi da gurfanar da su gaba kuliya.

Rundunar ta kara kira ga iyaye da su sa ido kan mu’amular da ‘ya’yansu suke yi domin rage matsalolin yawan shiga kungiyar asiri a Jihar.