✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Kasuwar Kayan Gwari ta Zuru suna neman dauki

Kasuwar Tumatur ta garin Zuru da ke Karamar Hukumar Zuru a Jihar Kebbi ita ce kan gaba a jerin kasuwannin da ke taka rawa wajen…

Kasuwar Tumatur ta garin Zuru da ke Karamar Hukumar Zuru a Jihar Kebbi ita ce kan gaba a jerin kasuwannin da ke taka rawa wajen samar da tumatir da ake amfani da shi a kasashe da dama na Afirka.

A ziyarar da Aminiya ta kai kasuwar, ta fahimci ana cin kasuwar ne a tsawon wata uku zuwa hudu a shekara kuma tana da tasiri sosai wajen samar da kayan miya da ake amfani da shi a duk fadin kasar nan.

Kasuwar tana samar wa dubban jama’a aikin yi, amma da ruwan sama ya sauka shi ke nan sai harkoki su tsaya a kasuwar sai kuma badi. Duk da yake a kowace rana kasuwar tana hada wa Gwamnatin Jihar Kebbi da Karamar Hukuma kudaden shiga masu yawa, kuma sama da mutum dubu biyar na cin abinci a cikinta, amma har yanzu babu wani aiki da gwamnati ta yi na taimakon masu kasuwancin, kullum sai dai alkawura da ba a cikawa.

Binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa kasuwar ta kwashe fiye da shekara 35 tana ci, tun lokacin Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Shehu Kangiwa wanda ya kaddamar da shirin noman rani a yankin Zuru da Yawuri da hadin gwiwar kasar Rasha. Sai dai gwamnatocin da suka biyo baya ba su yi wani abin a zo a gani ba don sake ingantawa da bunkasa noman rani a yankin. Har yanzu gwamnati ba ta samar da hanyoyi ko kuma bullo da wata hanya da za a rage wa manoma da ’yan kasuwa irin dimbin asarar da suke yi a kowace shekara ba, sai dai amsar kudin haraji da suke yi.

Kasuwar ta hana zaman daba, da bangar siyasa da kuma zaman kashe wando a tsakanin matasa, ta hanyar samar wa matasa ayyukan yi da dogaro da kai kamar yadda Boka Dan Zuru da Umaru Magaji da suke aikin dako da lodi a kasuwar suka shaida wa Aminiya. Sun ce suna loda akalla mota 50 a kowace rana, “Muna jin dadin yadda muke gudanar da aikinmu, muna da kungiyar da ke kula da aikin da muke yi.

“Mun kai akalla mutum 300 da muke yin lodi a wannan kasuwar. A kungiyarmu muna da lambobi har 5, kuma akwai mutum 60 a kowace lamba, idan za a yi lodi sai a kira lamba wadanda ke karkashin wannan lambar sai su zo su yi.” inji su.

Alhaji Inuwa Mai Ata shi ne Shugaban Masu Kasuwancin Tumatir na kasuwar, ya shaida wa Aminiya cewa a kowace shekara gwamnati tana yi musu dadin baki cewa za ta tallafa musu, amma kuma har yanzu ba su gani a kasa ba, inda ya nuna cewa tattalin arzikinsu ya riga ya karye. “Da ina iya loda motoci da yawa in tura Kudu, amma yanzu abubuwan duk sun tabarbare kuma gwamnati ba ta dube mu da idon rahama ba. Muna bukatar taimako sosai daga gwamnati,” inji shi.

Wani babban manomin atarugu da tumatir wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun tafka asara fiye da yadda ake tsammani, domin a cewarsa Kasuwar Birnin Kebbi da ta kone, an hango hayaki, “Amma mu ba a ganin asarar da muke yi don haka ma ba a damu da ita ba. Mun amsa kiran da gwamnati ta yi mana na mu yi noma domin a ciyar da kasa gaba. A bara na kashe Naira miliyan daya da rabi wajen noman atarugu da tumatir, amma ko dubu 50 ban iya hadawa ba. Yanzu da kake gani na karye, na rasa jarin da nake amfani da shi,” inji shi.

Manomin ya ce gwamnati ba da gaske take yi ba wajen kawar da matsalolin da manoman suke fuskanta, “Ba zan ce gwamnati ba za ta iya ba amma gaskiya ba da   gaske take yi ba. Akwai mutane sama da dubu daya da suke cin abinci a karkashina, amma ban taba samun tallafin Naira dubu 10 daga wajen gwamnati ba,” inji shi.

Ya ce a yanzu manoma tumatir na cikin halin damuwa sosai fiye da kowane lokaci a baya, “A da muna da kamfani 18 da ke sarrafa tumatir a Arewa, amma yanzu sai guda daya ne yake aiki, shi ma ba kowane lokaci ba.” Na kai tumatir dina kwando 560 kamfanin amma sai da ya kwana bakwai ba a juye ba lokacin da aka zo kaina, ya rube, sai dai zubarwa aka yi,” inji shi.

Madam Justina John da aka fi sani da Maman Sunday, ’yar kabilar Ibo ce ’yar asalin Jihar Imo da ke sayar da abinci  a Kasuwar Tumatir ta Zuru cewa ta yi, “Na fi shekara 30 ina sayar wa ’yan uwana Ibo da ke zuwa da kwando ko sayen kayan gwari abinci. Kasuwar nan ita ce cibiyar kayan gwari na yankin Arewa maso Yamma da ma kasar nan. In dai kana son samun kayan gwari mai kyau, sai ka zo Zuru domin har kasar waje ana fita da shi.”