✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan kasuwar Jos sun koka da Hukumar Kwastam

Wasu ‘yan kasuwa da ke kasuwanci a Kasuwar ‘Yan Kwalli da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato sun bukaci Shugaban Hukumar Kwastam ta kasa…

Wasu ‘yan kasuwa da ke kasuwanci a Kasuwar ‘Yan Kwalli da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato sun bukaci Shugaban Hukumar Kwastam ta kasa Kanar Hameed Ali kan ya yi bincike kan shinkafa da man gyadarsu da aka kama mota uku a kan hanyar Saminaka zuwa Jos, a kwanakin baya.
Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari, mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta karamar Hukumar Jos ta Arewa Alhaji Habibu Lawal Nalele ya bayyana cewa jami’an hukumar sun kamawa ‘yan kasuwarsu buhunan shinkafa da man gyada mota uku. “Bayan da suka sayo a Kano suna dawowa a kan hanyar Saminaka zuwa garin Jos,” inji shi.
Ya ce “wannan kamu da jami’an suka yi wa kayayyakin ‘yan kasuwarsu, wani babban abin takaici ne, domin  wadannan kayayyaki’yan kasuwar namu sun sayo su ne daga kasuwa.”
Ya ce da wuya ka ga karamin dan kasuwa ya je waje ya sayo shinkafa,  kamfanoni ne suke zuwa su yo odar shinkafa daga waje.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin hukumar ya ci tura.