Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar wajabta yin gwajin jini kafin yin aure a Jihar Kano.
Sabuwar dokar wacce za ta fara aiki daga ranar 13 ga watan Mayun shekarar da muke ciki, ta wajabta wa masoya yin gwaje-gwajen na jini, da ciwon hanta, HIV, amosanin jini da sauransu kafin a daura aure.
- Maganin Gargajiya Ya Kashe Mutum 2, Wani Na Asibiti A Ondo
- Abinci Ya Yi Ajalin Mutum 1 Wasu 75 Na Asibiti A Saudiyya
“Dokar daya ce daga cikin matakan da muke dauka domin tsaftace harkar aure a Kano da kuma kiyaye lafiyar ’ya’yanmu na gaba.
“Muna tabbatar muku da cewa duk dan da za a haifa a jihar nan gaba, zai zo ne lafiya mai inganci,” in ji gwamnan.
A nasa bangaren kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya ce baya ga bai wa ’ya’yan da za a haifa nan gaba a jihar kariya, dokar za ta tabbatar da babu wanda aka cuta a lokacin aure tsakanin mijin da matar.
Ya jaddada cewa ba iya gwaje-gwaje kawai dokar ta tilasta ba, har da hana nuna kyama ga masu cutar AIDS, amosanin jini, ciwon hanta da sauran larurori irinsu.
“Duk wanda muka samu da karya wannan dokar, za a ci shi tarar Naira dubu 500 daurin shekaru biyar ko ma duka biyun,” in ji shi.