✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan kasuwan da gobara ta shafa sun shiga mawuyacin hali’

Hadaddiyar kungiyar ‘Yan Koli ta Najeriya ta bukaci gwamnatocin jihohin arewa su tallafawa kananan ‘yan kasuwar da suka yi asara, a gobarar da  aka yi…

Hadaddiyar kungiyar ‘Yan Koli ta Najeriya ta bukaci gwamnatocin jihohin arewa su tallafawa kananan ‘yan kasuwar da suka yi asara, a gobarar da  aka yi a wasu kasuwanni da ke jihohin arewa a kwanakin baya.
Shugaban kungiyar Alhaji Usman Baba Sa’idu ne ya bayyana wannan bukata a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce  tallafawa kananan ‘yan kasuwar da wadannan gobara ta shafa ya zama wajibi musamman idan  aka dubi irin mawuyacin halin da suke ciki a yanzu, sakamakon irin dimbin asarar da suka yi. Ya ce a wadannan gobara da aka yi a kwanakin baya  Kano da  Kebbi da Abuja da Sakkwato da Mararraba da ke Jihar Nasarawa  duk kananan ‘yan kasuwa ne suka fi yin asara. Kuma suna nan sun zama abin tausayi, saboda dimbin asarar da suka yi.
Har ila yau, ya ce  don haka ya kamata gwamnatocin jihohin da wadannan masifu  suka auku su tausayawa wadannan kananan ‘yan kasuwa, ta hanyar tallafa masu. Kuma su tsaya wajen ganin tallaffin da za su bayar, ya isa zuwa ga kananan ‘yan kasuwan.
Daga nan ya yaba wa Gwamnan Jihar Filato Simon Bako Lalong kan sanya hannun da ya yi a aikin sake gina babbar kasuwar Jos da ta kone shekaru 12 da suka gabata. Ya ce babu shakka wannan mataki da gwamnan ya dauka zai yi matukar taimaka ‘yan kasuwa tare da farfado da harkoki.