’Yan kasuwan Amurka da takwarorinsu na Najeriya sun ta karrama tsohon Gwamnan Jihar Kano a zamanin mulkin soja, Kanar Dr. Sani Bello (Mai ritaya).
Cibiyar Kasuwanci ta Najeriya da Amurka (NACC) ta karrama Kanar Sani Bello, wanda shi ne Shugaban Kamfanin Makamashi na Mainstream Energy Solutions (MESL) da gidan Talabijin na Qausain, ne a yayin bikin cikarta shekaru 65.
NACC wadda ke ci gaba da jajircewa wajen inganta dangantakar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Najeriya da Amurka, ta yaba da jagorancinsa ga kwararrun ’yan kasuwa da kuma muhimman gudummawarsa a harkokin kasuwanci, makamashi da kuma yada labarai a Najeriya.
A karkashin jagorancinsa, Kamfanin Makamashi na MESL ya gudanar da manyan tashoshin samar da wutar lantarki kamar Kainji, Jebba, Zungeru, da Kashimbila, yayin da Gidan Talabijin na Qausain yake ci gaba da bunkasa a fannin yaxa shirye-shirye.
Bikin ya kuma gabatar da naxin Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban majalisar na kasa karo na 20.