✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwa sun yi alkunutu saboda masifar da suke funskanta a Legas

’Yan Kasuwar Kayan Gwari ta Ilepo da ke Abgado Oke-Odo a Jihar Legas sun gudanar da addu’o’in Alkunutu saboda masifar da ta taso musu a…

’Yan Kasuwar Kayan Gwari ta Ilepo da ke Abgado Oke-Odo a Jihar Legas sun gudanar da addu’o’in Alkunutu saboda masifar da ta taso musu a kasuwar na kamen shugabannin kasuwar su 7 da suka hada da Shugaba da Sakatare da ’yan sanda suka kame a yammacin Juma’ar makon jiya.

Limamin da ya jagoranci addu’o’in Alkunutu Malam Muhammadu Buhari ya shaida wa Aminiya cewa sun shirya addu’o’in Alkunutu ne bisa koyarwar Sunnar Manzon Allah (SAW), wanda ya umarci al’ummarsa cewa duk lokacin da masifu suka dame su, to su gudanar da addu’o’in Alkunutu domin samun sauki daga Allah. “Alal hakika masifar da muka samu kanmu a Kasuwar Ilepo na kame mana shugabanni babba ce, domin duk al’ummar da aka kame shugabanninta an dauko hanyar rusa ta ce, saboda al’amura ba sa tafiya daidai ba tare da shugabanci ba. Kuma duk al’ummar da ta sanya ido ana wulakanta shugabanninta, za ta lalace don haka muka yanke shawarar yin addu’ar a duk lokacin da muka yi Sallah tun daga ranar Litinin da ta gabata. Muna fatan Allah Ya yi mana maganin duk wanda ke da hannu a wannan lamari,” inji shi.

Alhaji Ali Ladan Madobi Shugaban ’Yan Albasa a Kasuwar ta Ilepo ya shaida wa Aminiya cewa ’yan kasuwar suna cikin zullumi ganin yadda aka kame shugabanninsu aka garkame su kusan mako guda. “Haka siddan wadansu bara-gurbin mutane suka hada kai da ’yan yuniyan da ke karbar Naira dubu shida daga duk motar da ta dauko kaya daga Arewa ta sauke a kasuwar, sun hada kai da Shugaban karamar hHkumar Agbado Oke-Odo suna tayar mana da hankali. Sun hada baki suka yi sharri ga shugabannin suka alakanta su daga mutuwar wani dan yuniyan, wanda ya sha giya ya mutu yau kimanin wata 8. Sai yanzu za su alakanta shugabannin da mutuwarsa saboda ba su da makama, muna biyan dukan hakokkin gwamnati kuma gwamnatin Jihar Legas ba ta da masaniya a kan abin da ake yi mana, ta aminta da kasuwar illa shugaban karamar hukuma ne yake neman mu da masifa, yana so ya rushe kasuwar ya sake gina rumfuna ya sayar domin son zuciyarsa. A baya ma ya yi irin haka, fatanmu shugabannin kasar nan su yi mana adalci su shigo cikin wannan lamari,’ inji shi.  

Har zuwa hada wannan rahoton ba a sako shugabannin kasuwar ta Ilepo ya, kuma duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin bangaren karamar hukuma ya ci tura.