✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwa sun koka game da rufe kasuwa a Kano

A cikin makon jiya ne wasu masu sayar da rake suka koka game da hana su gudanar da kasuwancinsu a kasuwar ‘yan Rake da ke…

A cikin makon jiya ne wasu masu sayar da rake suka koka game da hana su gudanar da kasuwancinsu a kasuwar ‘yan Rake da ke unguwar Darerawa a yankin Rijiyar Lemo cikin karamar Hukumar Fagge ta Jihar Kano.
Sai dai kuma a daidai lokacin da masu sayar da raken suke wanann korafi, a bangare guda Mai unguwar  Darerawa ne yake dora alhakin tashin nasu a kan mazauna unguwar wadanda suka yi karar masu sayar da raken gaban wata kotu  game da irin abubuwa na “gurbacewar tarbiyya da kazanta da masu sayar da raken ke haifarwa ga jama’ar unguwar.”
‘Yan kasuwar wadanda suka bayyana cewa sun shafe tsawon shekaru 36 suna gudanar da kasuwancinsu a wanann kasuwa sun koka game da yadda rufe kasuwar ya jawo musu toshewar hanyar samun abincinsu.
Shugaban ‘yan kasuwar raken Malam Sani Liman ya shaida wa Aminiya cewa “ba mu kadai rufe kasuwar ya tsungunar ba, har da masu abinci da sauran matasa da ke samun abin kai wa bakin salati a wanann kasuwa,” inji shi.
Kodayake, ‘yan kasuwar sun zargi Mai unguwar da hadin baki da Alkalin kotun majistare don rufe musu kasuwar saboda sun ki amincewa da bukatarsa, inda suka ce “ya nemi su kara masa wani kudi a cikin abin da suke ba shi na goro a duk karshen wata.”
Aminiya ta fahimci cewa wata kotun majistare da ke Jihar Kano ce ta umarci masu sayar da raken a wanan kasuwa da su bar wanann wuri sakamakon korafe-korafe da mutanen yankin suka kai gaban kotun.
Yayin da Aminiya ta tuntubi Mai unguwar Darerawa Malam Musa Ibrahim ya musanata zarge-zargen da masu sayar da raken suke masa, inda ya jaddada cewa rufe kasuwar ya biyo bayan korafe-korafen da mazauna yankin suka yi a gaban kotun. Ya ce “Ni babu wanda yake ba ni kudi a cikinsu ballantana na nemi karin wani abu a kai, magana ce mazauna unguwa suka same ni cewa ba su jin dadin yanayin da ake gudanar da harkar rake a unguwar kasancewar kasuwar tana jawo musu kazanta a unguwar ga kuma yadda tarbiyyar ‘ya’yansu ke barazanar lalacewa. Baya ga haka kuma idan aka kone bawon raken tokar kan shiga gidaje ta haifar wa da jama’ar wurin cutuka ga iyalansu,” inji shi.