✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasar Lebanon mazauna Kano sun samar da asibiti na zamani

za a yi bikin kaddamar da shi, bayan kammala daukar sabbin likitoci

’Yan kasar kasar Lebanon mazauna Kano sun samar da wani asibiti na zamani a babban birnin jihar.

Hakan ta bayyana ne lokacin da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kai ziyarar gani da ido ranar Litinin a unguwar Bompai, a cewar Jami’in yada labarai na fadar, Balarabe Kofar Na’isa.

Asibitin na dauke da gadajen kwanciya 25, an kuma samar da na’urori na zamani domin gwaje-gwajen cututtuka, baya ga wurin kabar haihuwa, da kuma kula da jarirai.

Sarkin Kano ya yi murna da samar da asibiti , a matsayin wani babban cigaba da ya zo wa al’ummaar jihar.

Sannan ya ce, asibitin zai rage yawan fita waje da ’yan Najeriya ke yi domin neman magani.

A jawabin shugaban asibitin, Abbas Hajaaj ga sarki a yayin ziyarar, ya ce sun samar da asibitin ne domin kishin jihar, an kuma sa masa suna asibitin ’yan Najeriya da ’yan Lebanon.

A cewarsa, nan ba da dadewa ba za a yi bikin kaddamar da shi, bayan kammala daukar sabbin likitoci da ma’aikatan jiyya da na gudanarwa.