✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan jaridar bogi sun shiga hannu kan damfara da ‘transfer’ ta bogi

Sun tura wa mai kaya alat na bogi na N33,00 a matsayin kudin buhun shinkafar da suka saye

An cafke wasu mutum biyu da ke karyar su ’yan jarida ne a Jihar Kano bisa zargin damfarar wani dan kasuwa buhun shinkafa ta N33,000.

’Yan sanda sun ce su biyun sun kirkiri sakon shigar kudi na bogi na  N33,000 inda suka yi amfani da shi wajen biyan buhun shinkafar da suka siya wajen wani mai shago a Rukunin Gidajen Sharada, cikin Karamar Hukumar Birni da Kewaye a Jihar Kano.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a ranar Laraba.

“Bayan samun rahoton abin da ya faru, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano, CP Mamman Dauda, psc(+) ya ba da umarnin gudanar da bincike karkashin jagorancin SP Abdulrahim Adamu inda a karshe aka damke masu laifin.

“Yayin bincike an gano wadanda ake zargin dauke da katin shaidar aiki (ID Card) na Gidan Rediyon Vision FM, Kano,” in ji Kiyawa.

Bayanan ‘yan sanda sun nuna wadanda ake zargin sun tafi har Gidan Rediyon Vision FM a Kano suka sato katin shaidar aikin da suke amfani da shi.

“Kuma sun amince kan cewa sun tafi shagon sun sayi buhun shinkafa inda suka yi tiransfa ta karya,” in ji jami’in.

Ya ce Kwamishina ya ba da umarnin a tura batun Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar don zurfafa bincike.

“Za a kai wadanda ake zargi kotu bayan kammala bincike,” in ji Kwamishina.

Kwamishinan ya bukaci jama’a su lura da ‘yan damfara da ke yawo suna cutar mutane ta wannan mummunar hanyar.

%d bloggers like this: