’Yan Jam’iyyar PDP sun yi zanga-zanga a ofishin jam’iyyar ta kasa bisa zargin muna-munar a taron jam’iyyar na Kananan Hukumomin Jihar Neja.
Musa zanga-zangar na zargin kwamintin jam’iyyar na kasa da ya gudanar da zaben da bayar da kai bori ya hau a zaben da aka yi a a lokacin taron.
- Shigo da masara: Matasa sun caccaki gwamnati
- ‘Yan sanda sun mika wa iyalai Naira miliyan hudu da aka tsinta
- Sojoji sun bindige dan ta’addan Binuwai ‘Gana’
Sun yi zargi cewa kwamitin karkashin jagorancin Sanata Misau da ’yan tawagarsa sun bari an yi magudi a zaben na karshen makon da ya gabata.
Masu korafin wadanda tsohon dan takarar gwamnan jihar Umar Nasko ya jagoranta sun bukaci Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na kasa ya share musu hawaye.
Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Umar Tsauri, a jawabinsa ga cincirindon masu zanga-zangar da suka mamaye kofar shiga hedikwatar jam’iyyar ya yi alkawarin duba kokensu, kafin daga baya su watse.