Sojojin Najeriya sun tsare wasu mayakan kungiyar Boko Haram da suka mika wuya tare da iyalansu a Jihar Borno.
Wasu mayaka su tara da suka mika wuya a kauyen Ruwaza da ke Karamar Hukumar Bama ta Jihar tare da iyalansu kananan yara mata 22 da manyan mata 10, suna hannun dakarun Bataliya ta 202.
- An kama mai garkuwa ya je banki ciro kudin fansa
- An kama matashi da bindigogi da rigar Fulani a Kafanchan
Daraktan Yada Labaran Rundunar, Birgediya Onyema Nwachukwu, ya ce iyalan mayakan na ISWAP sun kuma hada da manyan mata 15 da kananan yara mata 26.
Ya ce sojoji da ke aiki a kan hanyar BoCobs zuwa Bama sun tsare wasu ’yan Boko Haram 20 da suka mika wuya tare da iyalansu a kauyen Nbewa na Karamar Hukumar ta Bama.
“Duk wadanda ake zargin sun mika wuya ga sojoji ne a lokacin sharar da sojojin suka yi ranar 29 ga watan Yuli a yankin.
“An yi wa kananan yaran allurar rigakafin cutar shan-inna, manyan kuma, maza da mata, an tantance su ana yi musu tambayoyi,” inji shi.
Nwachukwu ya kara da cewa sojojin Bataliya ta 73 tare da mafarauta da ’yan ‘Civilian JFT’ sun kama wani mai kai wa ’yan ta’adda man fetur a kan hanyar Molai zuwa Damboa yana cikin shirya yadda zai kai wa ’yan ta’addan da ke cikin daji wasu kaya.
An kama mutumin da jarkokin man fetur da na injin oyil da oyil tritmen sai cocila da gidajen sauro da dardumomi da barguna da kuma fakiti 10 na batura da sufanoni da shalisho dozin uku.
“Akwai kuma kayan abinci da biskit fakiti biyar da kuma fakiti biyar na sinadarin dandano,” inji shi.