Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa ta samu nasarar tarwatsa wani gungun bokaye da suke fakewa da sunan su malaman rukiyya ne a kasuwar Shuwarin da ke karamar Hukumar Dutse, inda bokayen suka gudu suka bar kayansu a kuma aka kama daya daga cikinsu.
Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar, Malam Ibrahim dahiru Garki ya ce bokayen suna fakewa da sunayen Allah suna karance-karance, a ranar kasuwa suna amsar Naira dari a wurin jama’a, suna ba su bayanan karya a kansu.
Ya ce kamar yadda suka samu korafe-korafe daga jama’a, bokayen sun jima suna damfarar mutanen kauye a ranakun kasuwar garin Shuwarin inda suke yi wa mutane duba idan kayansu ya vata ko idan suna neman aure. Ko idan mutum yana jinya, su ce mayu ne suka kama shi, lamarin da yake haifar da tashin hankali a tsakanin al’umma.
Ya kara da cewa sun kama daya daga cikinsu mai suna Muhammad Bello a lokacin da yake aikinsa na bokanci a kasuwar, amma ya tabbatar wa Hisba cewa ya daina shigowa Jihar Jigawa da sunan ya yi wata harka ta bokanci, ya tuba ya daina kuma ya amshi nasihar hukumar.
A gefe daya kuma rundunar ta Hisba ta raba wa yara maza da mata da iyayen marayu mata da nakasassu sabbin suture, a kokarinsu na tallafa wa marasa karfi da rangwamen gata.
Daga cikin wadanda suka amfana dinkakkun kayan, akwai yara mata 100 da yara maza 100, yayin da masu bukata ta musamman mutum hamsin, aka raba masu yaduka da shadda, sai wani mutum daya aka ba shi keken guragu. Su kuma mata masu bukata ta musamman da iyayan marayu su 150 su ma aka ba su atamfofi 150 domin dinkawa.