✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan gudun hijirar Rohingya 17 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Myanmar

Mutanen na kan hanyarsu ce ta gudun hijira zuwa Bangladesh

’Yan gudun hijirar Rohingya akalla su 17, ciki har da kananan yara, sun rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin ruwan da ya ritsa da su a kasar Myanmar.

Rahotannin daga yankin Gabar Tekun kasar sun ce, hadarin jirgin ya auku ne sakamakon rashin kyawun yanayi.

Jirgin ruwan, mai dauke da mutum 90 na kan hanyarsa ta zuwa Bangladesh ne inda ya ratsa ta Bengal kana daga bisani ya nitse.

Rahotanni sun ce ruwa ya turo wasu gawarwakin zuwa bakin ruwa a yankin Rakhine, sannan fasinjoji sama da 50 sun bata.

Daruruwan Rohingyawa, wadanda galibinsu Musulmai ne, ke hijira suna barin Myanmar zuwa Bangladesh saboda muzguna musu da sojojin kasar ke yi.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kadauwarta dangane da hatsarin.