✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan gudun hijirar Najeriya dubu 40 na cikin tsaka-mai-wuya a Kamaru

Lokacin da kungiyar Boko Haram ta rika kai munanan hare-hare a garin Rann, hedikwatar Karamar Hukumar Kala-Balge da ke Jihar Borno, akasarin mutanen garin sun…

Lokacin da kungiyar Boko Haram ta rika kai munanan hare-hare a garin Rann, hedikwatar Karamar Hukumar Kala-Balge da ke Jihar Borno, akasarin mutanen garin sun kaurace masa zuwa Goura da ke kasar Kamaru. Sai dai  kuma a yanzu haka hukumomin tsaro sun tabbatar da cewar hankali ya kwanta a garin na Rann kuma mutane za su iya komawa inda kuma hukumomin kasar nan suka tanadi yadda ’yan gudun hijira da yawansu ya kai dubu 40 za su iya komawa garin Rann.

Aminiya ta samu bayanin cewa akasarin ’yan gudun hijirarba su son dawowa garin Rann saboda suna tsoron kada ’yan Boko Haram su sake kawo musu hari ba zato ba tsammani.

Bayanai sun ce hukumomin Najeriya da Kamaru suna tattauna yadda za a komo da ’yan gudun hijirar daga kasar Kamaru duk da tsoron da suke nunawa kan rashin tabbas a harkar tsaron da kuma rashin isassun kayan bukatun yau da kullum da suka hada da abinci da tsabtataccen ruwan sha da sauransu da ka iya jawo kamuwa da cututtuka musanmman ga kananan yara da mata da za su iya haifar da matsalolin rayuwa ga  ’yan gudun hijirar.

Kungiyar Likitoci ta Nagari-Na-Kowa (Doctors Without Borders) ta jan hankalin hukuumomin Najeriya cewa kada a yarda a dauko wadannan mutanen a yanzu, domin akwai barazanar tsaro da yiwuwar kamuwa da  cututtuka, baya ga rashin isasshen abinci da ruwan sha da kayayyakin masarufi.Ta ce maimakon haka, a ci gaba da rike su a kasar Kamaru zuwa wani lokaci, gudun kada a yi gudun zago a fada wa gara.

To amma wani jami’i a Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Malam Manga Salihu Danjuma, ya fada wa Aminiya cewa “Muna nan muna aikin hadin gwiwa a tsakanin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) da NEMA da Kwamitin PCNI gami da Hukumar Abinci ta Duniya (FAO), wajen samar da ingantattun kayayyakin masarufi da abinci da ruwan sha ga ’yan gudun hijirar na Rann, kafin a dawo da su daga garin Goura ta kasar Kamaru. Don haka muke son mutanen su kwantar da hankalinsu wajen dawowa idan har hukumomin tsaro suka shirya komawarsu.”

Daga dukan alamu hukumomin tsaro sun shirya dawo da ’yan gudun hijirar su dubu 40, daga garin Goura a kasar Kamaru, abin da mutanen da abin ya shafa ke bukatar a daga musu lokaci don su samu su natsu daga fargabar da suka shiga ciki na hare-haren ’yan Boko Haram da kuma rashin samun kwanciyar hankali ta fuskar rasa ababen more rayuwa.

Mako uku da suka gabata ne wadansu ’yan bindigan da ake tsammanin ’yan Boko Haram ne suka kai wa mutanen garin Rann wani mummunan harin da ya hallaka jama’a da dama, abin da ya jefa da fargaba a zukatan al’ummar yankin, wadansu suka tsere zuwa kasar Kamaru, inda suka tsinci kansu cikin mawuyacin hali na rashin isasshen abinci da tsabtataccen ruwan sha da rashin abubuwan more rayuwa da kuma da rashin magunguna, a can garin Goura.

Akwai dai kungiyoyin agaji na duniya da suke iyacin kokarinsu wajen shawo kan wannan matsalar, to amma kungiyoyin sun tabbatar da cewa zamansu a garin Goura ya fi muhimmanci bisa a dawo da su garin Rann, saboda matsalar tsaro da tsaurin rayuwa; ganin cewa a kowane lokaci ’yan bindigar suna yawan kai musu hari, inda  ake rasa rayuka da dukiyoyi.