Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya karbi rukuni na biyu na karin ’yan gudun hijirar Najeriya su 885 da aka debo daga kasar Kamaru.
Jami’an gwamnatin Kamarun, wadanda Gwamnan Jihar Arewa Mai Nisa da ke kasar, Mijinyawa Bakari ya jagoranta, ne suka damka mutanen a yayin wani kwarya-kwaryar biki da aka yi a birnin Maroua ranar Talata.
- Dan sanda ya ki karbar cin hancin N1m don sakin mai satar mutane a Kano
- Sabbin kudi: Makiyaya sun roki Buhari ya kori Gwamnan CBN
Da yake gabatar da mutanen, Gwamna Bakari ya kuma damka musu tallafin wasu kayayyaki da na abinci, inda ya ce jimlar mutanen da aka dawo da su a yanzu ya kai 1,300.
Gwamna Zulum, a madadin gwamnatin Najeriya, ya yaba wa Shugaban Kasar ta Kamaru, Paul Biya, saboda daukar nauyin ’yan gudun hijirar tsawon shekara tara.
Shugaban riko na Karamar Hukumar Bama, Grema Terab, ne ya karbi mutane 855 din da aka dawo da su a wani gari da ke kan iyaka a kusa da Banki.
’Yan gudun hijirar dai sun zauna ne a sansanin Minawao.
Kowanne daga cikinsu ya samu gudunmawar N40,000 daga gwamnatin Najeriya da buhun shikafa mai nauyin kilogiram 50 da buhun wake mai nauyin kilogiram 10 da man girki lita biyar da kuma katan din magi da kuma kudi N60,000 daga gwamnatin Jihar ta Borno.
Ofishin Kula da ’Yan Gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) a kasar Kamaru wanda Uwargida Kimberly ta wakilta, ta ziyarci sabbin gidajen da aka gina a Banki, ta yaba wa Gwamna Zulum.
“Wannan abin burgewa ne, kuma haka ake bukata wajen magance kalubalen da ’yan gudun hijira ke fuskanta,” in ji ta.