Wasu ’yan gudun hijira akalla 6,500 da ke zaune a sansanin da ke Kwalejin Larabci da ke Maiduguri sun gudanar da zanga-zanga a babban titin Maiduguri zuwa Jos a ranar Talatar da ta gabata, inda suka haddasa cinkoson ababen hawa.
Masu zanga-zangar da suke korafin rashin abinci a sansaninsu, sun fito daga matsugunin nasu ne, inda suka rufe babbar hanyar motar, suka rika bayyana cewa sun gaji da jana’izar ’ya’yansu da ke yawan mutuwa sakamakon yunwa da karancin abinci.
Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Usman Durkwa ne da sojoji tare da ’yan sanda dauke da makamai ne, suka lallashe su, har suka samu nasarar dakile zanga-zangar, suka hakura.
Wadansu daga cikin ’yan gudun hijirar sun bayyana cewa kofi daya na shinkafa ake ba su a tsawon wuni guda. Wani mutumin Marte, Mustapha Bulun, mai shekara 62 ya bayyana matsalar da suke ciki, inda ya ce: “Na yi wa ’ya’yana biyu jana’iza a wannan sansanin namu, kuma wannan mace-macen yaran ya faro ne wata biyu da suka gabata, jim kadan da kammala azumin watan Ramadan. Suna ba mu kofi daya ne na shinkafa ko masara ga iyali daya a rana. Shin ta yaya kofin shinkafa daya zai wadaci iyalin mutum daya?”
Mataimakin Gwamna ya roki masu zanga-zangar su yi hakuri, sannan ya ba da umarnin a rusa kwamitin da ke kula da raba abinci na sansanin. Da yake karin bayani ga ’yan jarida, ya ce gwamnati ta turo da manyan motoci dauke da kayan abinci zuwa sansanin na ’yan gudun hijira, domin ci gaba da ciyar da su yadda ya kamata.
’Yan gudun hijira sun yi zanga-zanga a Maiduguri
Wasu ’yan gudun hijira akalla 6,500 da ke zaune a sansanin da ke Kwalejin Larabci da ke Maiduguri sun gudanar da zanga-zanga a babban titin…