Kasar Qatar ta bayar da tallafin Dala 50,000 domin gina cibiyar ilimi a Sansanin ’Yan Gudun Hijira ta Wassa da ke Abuja.
Qatar ta kuma yi alkawarin taimakawa wajen gina wa ’Yan gudun hijira gidaje 600-600 a jihohi hudu domin inganta rasuwar ’yan gudun hijirar.
- Masu garkuwa da ni Fillancin kasar Nijar da Chadi suke yi – Wanda aka sace
- An gurfanar da Matashi saboda cizon Budurwarsa a Mama
- Zamfara: An cafke mahara a Fadar Sarkin Shinkafi
Da yake bayar da tallafin kudin, Jakadan Qatar a Najeriya, Mubarak AlMuhannadi, ya ce kasarsa za ta ci gaba da ba wa Najeriya gudunmuwa don saukaka wa ’yan gudun hijira halin da suke ciki, samar musu abin dogaro da kai da kuma kare martabarsu.
“Za mu taimaka wa Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira wurin samar wa masu gudun hijira muhalli, gina musu cibiyoyin ilimi, mayar da su masu dogaro da kansu, da kuma kare martabarsu,” a cewarsa.
Da yake karbar tallafin, Kwamishinan Tarayya na Hukumar, Sanata Basheer Mohammed, ya tabbatar wa Gwamnatin Kasar Qatar cewa za a yi amfani da kudaden da ta bayar ba tare da rufa-rufa ba.
“Cibiyar za ta samar da ingantaccen ilimin zamani, yaki da jahilci da kuma sana’o’in dogaro da kai ga kananan yara da matasa ’yan gudun hijira.
“Za kuma a yi amfani da ita a matsayin cibiyar wayar da kai game da lafiya da kyautata tunani,” inji shi.
Ya kuma kara yaba wa kasar ta Qatar bisan alkawarinta na taimaka wa Hukumar wurin gina wa ’yan gudun hijira gidaje a jihohi hudu.
Mohammed ya ce za a gina gidajen ne a jihohin Katsina, Zamfara, Borno Kuros Riba karkashin shirin Hukumar na RCP na gina wa masu gudun hijirar.
Ye ce hukumar ta ware filaye mai fadin hekta 50-50 a jihohin domin gina gidaje 600-600 masu dakuna uku a kowacce daga cikin jihohin.
Za kuma gina cibiyar lafiya, makarantu, ofishin jami’an tsaro, cibiyar koyar da sana’o’i, da kasuwa a unguwannin, wadanda za kuma su kasance kusa da gonaki.