✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan fashi sun kashe mutum shida a Kaduna

Wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari wani kauye da ake kira Komo a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, inda suka…

Wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari wani kauye da ake kira Komo a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum shida.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe takwas na daren ranar Litinin.

Wadanda aka harbe sun hada da:  Ibrahim Jatau da Bala da Makeri da Musa da Ado sai Gayan.

Daya daga cikin ’yan bangan Udawa ne ya shaidawa Aminiya lamarin, inda ya ce tuni an yi jana’izar wadanda suka rasu.

” ’Yan fashi sun harbe mutum shida a kauyen Komo gaba da Udawa da ke a karamar hukumar Chikun a daren ranar Litinin. Na san wasu daga cikin wadanda suka rasu tsawon shekara 30 da suka wuce. Yanzun nan muka dawo daga jana’izarsu,” in ji shi.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya kawo karshen wannan kashe kashe da ke faruwa a yankin na Chikun da Birnin Gwari.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan jihar ASP Mohammed Jalige ya ce, zai kira wakilinmu idan ya bincika yadda lamarin ya faru amma har ya zuwa aika labarin bai kira ba.