Mutum hudu sun mutu wadanda suka hada da wani jami’in soja da wata yarinya a safiyar jiya yayin da wasu ’yan fashi suka bude musu wuta a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
Daya daga cikin wadanda suka tsira, wani jami’i hukumar shigi da fici ya ce lamarin ya auku yayin da suka bar Kaduna da misalin karfe takwas na safe a kan hanyarsu ta zuwa garin Ilorin da ke jihar Kwara a jerin gwanon motoci bas uku na kamfanin Kwara Express inda suka fada komar ’yan fashin su kimanin 20 kusa da garin Palwaya da ke yankin Karamar Hukumar Birnin Gwari a cikin jihar Kaduna da misalin karfe 10 na safe.
Ya ce ’yan fashin sun ummarci motocin su tsaya amma sai direbansu ya yi kokarin gudu sai kawai suka bude musu wuta wanda ya yi sanadin mutuwar wani jami’in soja mai suna David Ejisoro da wata yarinya da kuma wasu mutum biyu da ba a san su ba da ke cikin motar.
Aminiya ta gano cewa ’yan fashin sun harbi yarinyar a kai mahaifiyarta kuma suka harbe ta a nono.
Ya ce tuni aka dauki gawarwakinsu zuwa asibitin Birini Gwari inda ’yar matar ta bayar da ummarnin a binne ta a Birnin Gwari bayan ta sanar da mijin matar.