Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ’yan fashi da makami sun kai hari Unguwar Maitama da ke Abuja.
Mutum daya aka samu ajali ya katsewa hanzali yayin harin da ’yan fashin suka kai harin Layin Gana da ke unguwar ta Maitama bayan sawun mutane ya fara daukewa.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Yaki Alkawurran Bogi A Zaben 2023
- Wadanda Suka Kashe Wani Mutum a Imo sun shiga hannu
Bayanai sun ce ’yan fashin sun harbe mutumin ne yayin da suka kai harin da misalin karfe 8:46 na dare a jiya Laraba.
Wani mazaunin unguwar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun harbe mutumin ne a lokacin da ya yi kokarin kai wa wani mutum dauki da masu ta’adar ke kokarin sanya shi cikin wata bakar mota kirar Prado SUV da karfin tuwo.
Ya maharan wanda ake zargi masu gakuwa da mutane ne sun ajiye motar a gaban wani gida mai lamba 44 a kan titin na Gana, inda a nan ne suka harbi mutumin a ka wanda nan take ya shura.
Majiyar ta ce maharan sun yi awon gaba da mutumin da suka yi kokarin dauka yayin da suka bar gawar mutumin da suka harba yashe a kan hanya.
A cewar majiyar, wannan shi ne karo na biyu da makamancin wannan lamari ke faruwa a kan titin na Gana a makonnin baya bayan nan.
Majiyar ta kara da cewa, kai komon da wasu bakin matasa ke yi a unguwar ba zai rasaba nasaba da faruwar wannan lamari ba.
Ya ce bakin matasa da ke yawace-yawace a unguwar galibi sukan kai hari shagunan sayar da magunguna da sauran manyan shagunan sayar da kayayyaki, lamarin da ya sanya a yanzu ’yan sanda suka kulla damar yi wa tufkar hanci.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa tuni suka baza komarsu ta cafke wadanda suka yi aika-aikar.
Adeh ta musanta cewa ’yan sanda ba sa wani katabus na sauke nauyin da rataya a wuyansu wajen samar da tsaro a manyan shagunan da ke yankin.