’Yan wasa da jami’an zakaran gasar Premier ta Najeriya wato kungiyar Kano Pillars sun jingine zuwa Owerri don fafatawa da kungiyar kwallon kafa ta Heartland FC, bayan da ’yan fashi da makami suka kai musu hari da rana a jiya Alhamis a Abaji da ke kusa da Abuja.
daya daga cikin ’yan wasan da harin ya fi shafa shi ne dan wasan gaba na Pillars, Gambo Mohammed wanda aka harba a dantsensa. Wani dan wasan Ubong Ekpai an sare shi sosai a kai, yayin da wasu ’yan wasa hudu ke jinyar raunuka daban-daban a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Lakwaja.
Kakakin kungiyar Idris Malikawa ya tabbatar wa jaridar PREMIUM TIMES ta Intanet da faruwar lamarin, inda ya ce, ’yan bindiga sun kai hari ga bas din da ke dauke da ’yan wasan ne da misalin karfe 1 na rana.
“Yanzu haka muna Lakwaja muna jinyar ’yan wasa da jami’anmu da suka samu rauni bayan ’yan fashi sun kai wa bas din da muke tafiya hari a Abaji a yau (jiya),” inji Malikawa.
Ya ce, ba zai iya cewa ko za su ci gaba da tafiyar don buga wasan a karshen mako ba, ko a’a inda ya ce yanzu batun lafiyar ’yan wasa da jami’ansu ne a gabansu.