A shekaranjiya Laraba ce wata dattijuwa mai kimanin shekara 75 da ke zaune a garin Badawa a yankin karamar Hukumar Gezawa, Jihar Kano ta hadu da fushin wadansu da ake zargin ’yan fashi ne, inda suka harbe ta tare da babban danta mai kimanin shekara 50.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na dare. Dattijuwar mai suna Hajiya Abu Haruna da danta Alhaji Yakubu Haruna wanda aka harba a kafa, suna karbar magani a Asibitin kwararu na Murtala Muhammad.
daya daga cikin ’ya’yanta, Lawal Sarka ya shaida wa Aminiya cewa ba su da masaniya sai suka ji an bude wuta a cikin gidansu, kafin su san abin yi har an harbi mahaifiyasu. Ya ce ’yan fashin sun yi awon gaba da kudin da ba a san yawansu ba.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya ce ita dattijuwar yankanta aka yi da wuka a ciki, yayin da shi kuma danta aka harbe shi a kafa. Ya ce Kwamishinan ’Yan sandan, Jihar Kano, Rabi’u Yusuf ya umarci Mataimakinsa Mai kula da Sashen Bincike ya kai ’yan sanda garin don samar da cikakken tsaro a yankin.