✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan fansho sun kai Gwamnatin Nasarawa Kotun Ma’aikata

Tsofaffin Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Nasarawa da suka yi ritaya su dubu 1,189 ne suka kai karar gwamnatin jihar kotun Ma’aikata da ke  Makurdi a Jihar…

Tsofaffin Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Nasarawa da suka yi ritaya su dubu 1,189 ne suka kai karar gwamnatin jihar kotun Ma’aikata da ke  Makurdi a Jihar Benuwai kan rashin biyansu kudaden giratuiti da ariyas na fanshonsu.

Da yake gabatar da takadar karar, a ranar Litinin lauyan mssu karar, Barista Sunday Okpale ya bayyana wa kotun cewa tun daga watan Satumban 2016 ne gwamnatin jihar take biyan ’yan fanshon rabin kudadensu tare da yi musu alkawarin za ta cika musu ragowar kudinsu daga baya, amma  har yanzu ba ta cika alkawarinta ba.

Ya ce bayan ’yan fanshon sun shigar da karar kwanakin baya a wasu kotuna da ke Lafiya a Jihar Nasarawa sai ya zamo wadanda ake karar da suka hada da gwamnatin jihar da hukumar fansho ta jihar da daraktan hukumar dukansu babu wanda ya halarci zaman kotunan ko sau daya kuma ba su turo wakilansu ba. Ya ce “Bayan mun fahimci cewa sun raina wadancan kotuna ne ya sa muka yanke shawarar dage karar daga Lafiya zuwa nan Makurdi don kotu ta bi musu hakkinsu.” Daga nan ya bukaci kotun ta gaggauta umartar wadanda ake kara su biya su hakkokinsu.

Alkalin Kotun, Mai shari’a Salisu Danjida ya dage zaman zuwa ranar 11 ga Fabrairun badi don ci gaba da sauraron karar.

Wakilinmu ya gana da daya daga cikin ’yan fanshon mai suna Alhaji Ibrahim Idris, inda ya nuna takaici kan cewa duk da kudaden da gwamnatin jihar ke samowa daga tarayya musamman na kulob din Paris da ya ce an bai wa gwamnatin jihar saboda biyan irin wannan bashi amma ta ki ta biya su hakkinsu.