Tsoffin ma’aikatan Hukumar Kula da Filayen Jiragen Saman ta Najeriya (FAAN) na barazanar rufe tashoshin jiragen saman saboda bambancin da ake nunawa wajen biyan su.
’Yan fanshon sun ba wa FAAN wa’adin ranar 4 ga watan Mayu, 2021, su magance matsalar, idan kuma suka ki, to za su fuskanci bore a fadin Najeriya.
- Matashi ya fille kan kakarsa ya kai ofishin ’yan sanda
- Tafsirin Ramadan: Izala ta tura malamai 500 zuwa kasashe
- Kano: Shugaban Karamar Hukuma ya nada mataimaka 55
- Dalilai uku na sauke Sufeto Janar Mohammed Adamu
Sun bayar da wa’adin ne a yayin wani gangami da Kungiyar ’Yan Fansho ta Kasa (NUP) ta gudanar a Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed (MMA) da ke Legas.
A ganawarsa da ’yan jarida, Sakataren Kasa na NUP, reshen FAAN, Kwamared Emeka Njoku ya zargi hukumar gudanarwar FAAN ta yi biris da dokar ka’idojin aiki da aka amince da yi a zaman da aka yi kan bambancin kudaden.