Wasu ’yan damfara ta intanet sun kirkiro shafin karya na ‘Daily Trust Hausa’ a dandalin sada zumunta na Facebook, inda suke yaudarar mutane tare da yin sojan gona da shi.
Shafin, wanda aka kwaikwayi shafin Aminiya da shi dai, ya jima yana kwafar labaranmu a matsayin nashi, sannan a lokuta da dama ya kan yada labaran da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
- Najeriya A Yau: Yadda Za A Bunkasa Fasahar Zamani Domin Samar Da Ayyukan Yi
- Ba da belin masu garkuwa na firgita mu — Mutanen Zariya
A kan haka, hukumar gudanarwar kamfanin Media Trust, mawallafa jaridun Daily Trust da Aminiya da kuma talabijin na Trust TV, na nesanta kansu da wannan shafin.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa shafin har ya fara wuce gona da iri inda har ya fara ba da kyaututtuka da kuma nada mutane a matsayin gwaraza.
Da yake tsokaci a kan lamarin, Babban Editan kamfanin na Media Trust, Naziru Mikail Abubakar, ya ce, “Wadannan mutanen sun fara wuce gona da iri, suna kwafar labaranmu, suna bayar da kyaututtuka ga mutane da sunanmu.
“Muna amfani da wannan kafar wajen jawo hankalin jama’a tare da nesanta kanmu da wannan shafin. Shafin kawai da Daily Trust ke da shi na Hausa a Facebook shi ne na Aminiya.
“Muna rokon jama’a su taimaka mana wajen wannan yakin da ’yan damfara ta hanyar ‘unfollowing’ dinsu, tare da kai rahotonsu ga shafin na Facebook don daukar matakin da ya dace,” inji Babban Editan.
Ya ce tuni suka aike da korafi a hukumance ga shafin na Facebook, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton, bai dauki mataki ba.
A yanzu haka dai, shafin na Daily Trust Hausa na da mabiya sama da 56,000, yayin da shi kuma na Aminiya ke da mabiya sama da 254,000.