✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan daba sun kai wa masu taron NNPP hari a Kano

Mutanen na kan hanyar taro Kwankwaso ne lokacin da aka kai musu harin

Wasu mahara da ba akai ga tantance su wane ne ba sun kai hari kan ayarin magoya bayan jam’iyyar NNPP a unguwar Na’ibawa da ke kan titin zuwa Zariya a Jihar Kano tare da kona motocinsu da dama.

Magoya bayan na NNPP dai na kan hanyarsu ce ta zuwa garin Kwanar Dangora da ke Karamar Hukumar Kiru a Jihar, domin taro dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda zai rufe taron yakin neman zabensa a Kano ranar Alhamis.

Yanzu haka dai bayanai sun nuna tuni Kwankwaso ya wuce garin na Kwanar Dangora a kan hanyarsa ta zuwa Kanon.

Akalla an kona motoci kimanin guda 10 kurmus, wasu da dama kuma an farfasa su.

A cewar wani ganau, mai suna Tasi’u Lawal, shi ma da kyar ya samu ya samu ya fito ta gilashin motar kafin ya tsira daga maharan.

“Alhamdulillah, na samu na sha da kyar. An fada mana dama suna can suna jiranmu, shi yasa muka yi birki a Na’ibawa, sai da muka taru da yawa kafin mu wuce.

“Kwatsam sai ganinsu muka yi suna fitowa ta ko’ina, suna kai mana sara da adduna, cikinsu kuma har da mata,” in ji Tasi’u.

Wakilinmu da ya ziyarci wajen ya ce yanzu haka an girke tarin jami’an tsaron da suka hada da sojoji da ’yan sanda da ’yan sibil difens, domin kwantae da tarzoma.

Kazalika, jami’an tsaron sun ce sun sami nasarar kama kimanin mutum 50 daga cikin wadanda ake zargi da hannu a kai harin.