✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan daba sun fille kan mutum sun buga kwallo da shi

’Yan sanda na farautar ’yan kungiyar asirin da suka yi wa mutumin kisan gilla.

’Yan sanda na farautar wasu ’yan kungiyar asiri da suka fille kan wani mutum suka buga kwallon kafa da shi.

’Yan kungiyar asirin sun yada bidiyon yadda suke ta kwallo da kan matashin da suka kashe din, wanda dan wata kungiyar asiri ne da ke hamayya da su.

Wani ganau ya ce ’yan kungiyar asirin sun yi wa mutumin kisan gilla ne bayan sun fito da shi da karfin tuwo daga cikin mota, suka harbe shi.

Daga baya sai suka sare kansa sun tafi da kan wani fili suna wasan kwallon kafa da shi suna masa izgili.

Lamarin ya faru ne a unguwar Igbariam da ke Karamar Hukumar Anambra ta Gabas a Jihar Anambra.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin ’yan sandan jihar Anambra, DSP Toochukwu Ikenga, ya ce “An harbe mutumin ne sakamkon rikicin kungiyoyin asiri da ba sa ga maciji.

“An tsaurara matakan tsaro kuma duk abin da aka gano za a sanar da mutane,” bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Anambra, Tony Olofu.