✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan daba sun far wa masu zanga-zangar Kaduna

’Yan daban sun rufe fuskokinsu suna jifan masu zanga-zangar

Wasu ’yan dabar da ake tunanin hayar su aka yi sun kawo hatsaniya wa zanga-zangar lumanar da Kungiyar Kwadago ta NLC ke yi a Jihar Kaduna.

Ganau sun ce a daidai lokacin da zanga-zangar ke gudana, wasu da ake zaton ’yan daba ne dau suka rufe fuskokinsu suna dauke da wukake da sanduna suka auka musu.

“Sun taho ne a cikin mota suka fara jifar ma’aikatan da ke macin da duwatsu; Mutane sun gudu sai dai masu zanga-zangar sun yi nasarar fatattakar su,” kamar yadda wani ganau ya shaida wa wakilinmu.

Sai dai har yanzu babu tabbacin kan wanda ya dauki hayar ’yan dabar domin su tarwatsa macin na lumana da ma’aikatan ke yi.

A yayin zanga-zangar, masu macin sun datse babbar hanyar garin na Kaduna, lamarin da ya tilasta masu ababen hawa sauya hanya.