✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan daba sun ƙone ofishin hukumar zaɓen Akwa Ibom

Rundunar ta tsaurara tsaro a ofishin hukumar domin tabbatar an yi zaɓen cikin lumana.

Wasu ’yan daba sun ƙone Ofishin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Akwa Ibom (AKISIEC), da ke karamar hukumar Ibiono Ibom.

Rundunar ’yan sanda jihar, ta tabbatar da kai harin, wanda ta ce an yi hakan ne domin hana gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

Da ta ke zantawa da manema labarai a Uyo a ranar Asabar, kakakin rundunar, ASP Timfon John, ta ce, “Wasu ’yan daba sun ƙone wani ɓangare na ofishin AKISIEC a Ibiono Ibom.

“Amma babu abin da ya samu kayan zaɓe, kuma ana ci gaba da gudanar da zaɓe.”

Ta ƙara da cewa, “Rundunar ta ƙara tsaurara tsaro a duk ofisoshin AKISIEC da wuraren da suka dace a jihar.”

Duk da harin, ’yan sanda sun tabbatar wa jama’a cewa duk cewar babu abin da ya samu kayan zaɓe, kuma ana ci gaba da zaɓen kamar yadda aka tsara.