Wasu gugun ’yan daba sun na rige-rigen dibar mai daga bututun man kamfanin NNPC da ke yoyo a Karamar Hukumar Amuwo-Odofin ta Jihar Legas.
Su ma masu sana’ar sayar da mai sun bi sahu wurin dibar man dizel din, inda kowannensu ke ta kai-komo da jarkoki.
- Gobara ta cinye kantuna 91 a kasuwar tufafi
- ‘Maganarmu ta karshe da dana kafin masu garkuwa su kashe shi’
Mutanen sun yi watsi da kashedin da Hukumar Agajin ta Kasa (NEMA) ta yi cewa man da ke yoyi na iya yin bindiga, amma ko a jikinsu.
Jami’in NEMA mai kula da shiyyar Legas, Ibrahim Farinloya ta yi kira mazauna unuguwar Abule Osun da ke daura da Festac a Karamar Hukumar Amuwo Odofin cewa su kaurace wa yankin, don su tsira da rayuwarsu.
Ya bayyana cewa wuta na iya tashi daga man da ke tsiyaya yana bi ta yankin.