✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Civilian JTF 1,000 sun rasu a yaki da Boko Haram —Kwamanda

Mayakan sa-kai na Civilian JTF akalla 1,000 suka rasu a yayin yaki da ta'addanin mayakan Boko Haram da ISWAP a Jihar Borno a tsawon shekara…

Mayakan sa-kai na Civilian JTF akalla 1,000 suka rasu a yayin yaki da ta’addanin mayakan Boko Haram da ISWAP a Jihar Borno a tsawon shekara tara a Jihar Borno. 

Babban Shugaban CJTF na jihar, Baba Shehu Abdulganiyu, ne ya bayyana haka a wurin taron koya sana’o’in dogari da kai ga wasu ’yan Civilian JTF 350 da kungiyar Tarayyar Turai da Hukumar Raya Al’adun Kasar Birtaniya suka dauki nauyi.

“Matsalar yaki da ta’addanci ya sa muka fito domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Borno kuma muna goyon baya da kuma taimaka wa jami’an tsaro wajen fatattakar ’yar tayar da kayar baya daga birnin Maiduguri.

“A wannan aiki, mambobinmu sama da 1,000 sun rasa rayukannsu a kokarinsu ya kare jihar, wanda hakan ya haifar da mata 1,000 da mazajensu suka rasu.

“Ba zan iya cewa ga hakikanin adadin mamatan namu ba, amma daga 2013 zuwa yanzu sun sun haura mutum 1,000.

“Byan matan akwai ’ya’yan  abokan aikin namu da suka rasa iyayensu, wadanda Gwamnatin Jihar Borno take tallafa wa.

“Amma iyalansu na bukatar karin tallafi, wanda kuma a shirye muke domin bayar da gudunmmawa a koyaushe.

“Kamar yadda muke ganin, gwamnatin jiha ita kadai ba za ta iya, ya kamata kungiyoyin jinkai su kawo dauki saboda muna da mambobin masu yawa da ke bukatar tallafi.

“Na yi amanna idan aka yi haka, zai ba wa jama’a karin kwarin gwiwa, kuma da yardar Allah, matsalar Boko Haram ta kusa zama tarihi,” in ji shi.

Babban Kwamandan na Civilan JTF ya bayyana cewa runduanr tana taiamaka wa sojoji da ’yan sanda da hukumar DSS da NSCDC da sauran hukumomin tsaro da ke yaki da ta’addanci da manyan laifuka.

Jami’in Shirin British Council, Emmanuel Iyaji ya ce hadin gwiwarsu da EU sun tsara shirin ne domin bunkasa tsarin hada kan mutanen jihar bayan matalsar Boko Haram.

Ya bayyana cewa bangarorin da aka horas da mambobin Civilian JTF din sun hada da gyaran kayan lantarki, kafinta, dinki, walda, hada takalma, aski da gyaran kai, hada burodi, sabulu, turaren wuta da na daki, da sinadaren kashe kwayoyin cuta.

Wani daga cikin masu koyar da sana’o’in kuma babban lakcara a Jami’ar Maiduguri, Dokta Waziri Zanna, ya ce shirin koyar da sana’o’in zai kara wa wadanda suka ci gajiyarsa hanyoyin samun kudaden shiga domin dogaro da kai.