✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan casu muka kama ba masu hada auren jinsi ba —Hisbah

Hisbah ta ce ta same su suna tsaka da aikata alfasha amma babu wata shaida da ke nuna auren jinsi suke hadawa

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta tabbatar da kama gungun wasu matasa maza da mata su 78 suna tsaka da aikata masha’a a wani gidan casu mai suna ‘White House’ a unguwar Nassarawa GRA.

Shugaban Hukumar, Harun Ibn Sina, ya shaida wa Aminiya cewa sun kama matasan ne bisa zargin aikata fasadi da kuma yin shiga ta bayyana tsiraici, amma ya karyata rade-radin da ke yawo cewan an kama matasan ne suna hada auren jinsi a tsakaninsu.

Ibn Sina ya ce, “Mun samu rahoto ne, amma da muka je wurin ba mu samu wata shaida da ke nuna cewa auren jinsi suke hadawa ba, amma duk da haka mun kama su saboda mun same su ne suna cikin aikata alfasha; A cikinsu akwai maza da mata.”

Ya kara da cewa matasan sun musanta cewa auren jinsi suke daurawa, shagalin bikin zagayowar ranar haihuwar dayansu suke yi.

Shugaban hukumar ya ce wadanda aka kama din suna tsare a hannun hukumar.