✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan boko ne matsalar Najeriya – Amaechi

Ya ce ’yan boko da ’yan siyasa ne ke kawo wa Najeriya koma baya

Ministan Sufuri kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Rotimi Amaechi, ya zargi manya-manyan ’yan bokon Najeriya da cewa sune matsalar kasar.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a bikin Ranar ’Yancin Yada Labarai ta Duniya da Kungiyar ’Yan Jarida ta Kasa (NUJ) ta shirya a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.

Matsalar kasar nan ba ta talakan da ke zaune a Akwa Ibom ko Ribas ba ce, ba ta mazaunin Kudu maso Gabas ko na Arewa ba ce. Matsalar ta ni da ku – ’yan boko – ce,” inji shi.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su dada kaimi wajen tabbatar da cewa ’yan siyasa sun yi abubuwan da ya kamata.

Amaechi, wanda kuma shi ne babban bako a wajen bikin ya ce matukar ba a fara bibiyar sahun abin da ’yan siyasa da ’yan boko suke yi ba, za a jima ba a ci gaba ba.

Ya ce ’yan boko na ta babatun sake fasalin kasa saboda babu sauran abin da za a yi kashe-mu-raba da shi.

“Da zarar ka ji ana maganar sake fasalin kasa, to babu shakka abin da ’yan boko fa ’yan siyasa za su raba ne ya tasar wa karewa. Saboda babu abin da za a raba ne, kasa ta fara fadawa kwata. Matsalar Najeriya ’yan boko ne ummul-aba’isunta, ciki har da ku,” inji shi.

Ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai da su jajirce wajen magance matsalolin kasar ta hanyar kawo rahotannin gaskiya a ayyukansu.