Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya koka cewa wadansu tsirarun ’yan boko da ke ganin dole sai sun ja akalar Najeriya na shirin waragaza kasar.
Ya ce halin da kasar ke ciki a yanzu na bukatar mahukunta su dauki matakan dawo wa da ’yan Najeriya kwarin gwiwa saboda akwai miyagu da dama a kasar.
- Aminanshi sun kashe shi kan bashin da yake bin su
- Hanyoyin da za a bi don magance matsalar tsaro —Janar Kukasheka
Da yake jawabin a ranar Litinin a Bauchi yayin bukin bude wani katafaren sansanin alhazai, sarkin ya ce, “Wadansu mutane na kai gwauro da mari domin ganin kasar ta wargaje.
“Na yi amannar cewa nauyi ya rataya a wuyanmu na mu tashi haikan mu kalubalanci wadannan tsirarun mutanen da ke ganin lallai sai sun tafiyar da akalar kasar nan.
“Ya kamata mu nuna wa talakawa cewa akwai rawar da za mu iya takawa, muna da hakki a kasar nan kuma babu wanda ya isa ya tursasa mu yin abin da yake so,” inji shi.
Sarkin Musulmin ya tunatar da shugabannin da kada su bari addu’ar wadanda aka zalunta ta kai ga Mahalicci domin hakan ka iya haifar da mummuna sakamako a kansu; saboda haka su yi wa talakawa adalci domin dalilin da ya sa aka zabe su ke nan.
Ya kuma hori ’yan jarida da cewa su guji yada labaran karya da ke iya haifar da tashin tashina a tsakanin al’ummomi masu addinai da kabilu mabambanta.