✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan boko ke ganin N5,000 ba za ta kawar da talauci ba —Sadiya

Mun shiga kauyuka kuma ga mutanen da idan aka ba su N5,000 har kuka suke yi, saboda ba su taba samun ta ba a rayuwarsu.

Ministar Agaji da Ayyukan Jinkai, Sadiya Umar Farouq, ta ce tunanin ’yan boko ne ke a ce N5,000 da Gwamnatin Tarayya take ba wa talakawa a wata-wata ta yi kadan ta fitar da su daga talauci.

Sadiya ta bayyana haka ne bayan an yi mata tambaya game da amfanin da N5,000 da gwamnati ke ba wa talakawa a duk wata a yunkurinta na fitar da ’yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci.

A cewarta, ma’aikatar da take jagoranta ganau ce kan yadda N5,000 din da ake biyan talakawa masu rauni a wata-wata ke taimakawa wajen fitar da su daga matsancin talauci.

“Idan aka lura, mutanen da aka ba wa N5,000 din tana da matukar muhimmacni a gare su, domin talakawa ne masu rauni, kuma tana kyautata musu rayuwa,” inji ta.

Sadiya ta yi wannan bayani ne ranar Alhamis a yayin yawabin mako-mako da Fadar Shugaban Kasa ta shirya.

Sai dai ta bayyana cewa amma akwai wasu ’yan Najeriya da N5,000 din ba ta kai yawan kudin katin da suke sanyawa a wayoyinsu ba.

“Irina da ku N5,000 ba ta kai kudin katin da muke sa wa a wayoyinmu ba —bambancin ke nan.

“Amma talakawa masu rauni na karkara har suna iya ajiye wani abu daga cikin N5,000 da ake ba su; Idan har kudin ba ya yi musu komai, ai tilasa su ake yi cewa su  rika yin adashin N1,000. Saboda haka N5,000 tana taimakawa.

“Gaskiya, duk mutumin da ya ce N5000 ta yi kadan, to wannan tunaninsa na ’yan boko ne, domin mu ganau ne, mun je yankunan karkara, mun kuma ga mutanen da idan aka ba su N5,000 har kuka suke yi, saboda ba su taba samun ta ba a rayuwarsu.

“Saboda haka kudin taimakawa wajen inganta yanayin rayuwarsu daga wani mataki zuwa wani wanda ya fi shi,” inji ministar.

%d bloggers like this: