Sakamakon hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa a Kudancin Jihar Yobe al`ummomin yankin na kaurace wa yankin saboda tsoron yiyuwar kungiyar za ta mamaye garuruwansu.
Mazauna garuruwan Goneri da Ambiya da Ngirbuwa da Muktum da Ambiya Gari da Katarko da Gujba da Buni-Yadi da Buni-Gari suna yin kaura sakamakon hare-hare da garkuwa da jama’a da ’yan Boko Haram ke musu.
Wani mazaunin Goneri ya bayyana wa Aminiya cewa jami`an tsaro sun kaurace daga yankin tun daga ranar da ’yan Boko Haram suka kai wa sansanin sojoji da ke garin Goneri farmaki. “Wannan ya ba ’ya’yan kungiyar damar shiga garin don kama duk wanda suke so, su kuma yi wa’azinsu a fili ba tare da tsangwama ba,” inji majiyarmu.
A garin Katarko mai nisan kilomita 21 daga Damaturu, inda mayakan kungiyar suka kashe mutum takwas, tare da sace wani baban malami mai suna Ali Sherrif da matarsa da wasu mutum biyu Goni Kolo da Is’hak Alhaji Goni, maharan sun farmaki sansanin sojoji ba su samu nasara ba, amma sun tarwatsa babbar gadar da ta hada Kudancin Yobe da sassan jihar ciki har da Damaturu. Kuma wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya ce tarwatsa gada cikas ce gare su wajen kai dauki a yayin da ’yan Boko Haram ke ci gaba da kai hare-haren ga wuraren.
A lokacin da maharan suka nufi Gujba kuma mutanen garin suka samu labari, hakimi da jama`a sun gudu, kuma wata majiya ta ce maharan sun kone asibiti da fadar hakimin da makaranta da sansanin jami’an tsaro da turakun wayoyin salula da gidajen sanannun ’yan siyasa da ma’aikatan gwamnati da masu hannu da shuni.
A Buni-Yadi, maharan sun sake kai farmaki ga sansanin soji, amma babu wanda ya karar da yadda abin ya kasance. Sai dai an ruwaito cewa mutanen garin suna ta yin kaura saboda tsoron abin da ka iya biyowa baya. Wani da ya yi kaura zuwa yankin Gombe ya ce mata da yara na yin kaura a kafa zuwa Gombe saboda karya gadar da ta hada su da Damaturu. “A kafa muke kaura, abin da zai ba ka tausayi sai ka ga mata da kananan yara na tafiya cikin daji ba su san inda za su ba. Ba abinci babu ruwan sha, wannan bala’i dame ya yi kama?” inji shi.
’Yan Boko Haram sun mamaye Kudancin Yobe
Sakamakon hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa a Kudancin Jihar Yobe al`ummomin yankin na kaurace wa yankin saboda tsoron yiyuwar kungiyar za ta mamaye…