Sama da gine-gine 30 ne ’yan Boko Haram suka kona tare da lalata amfanin gona da dama a wani hari da suka kai kauyen Wamdeo da ke Karamar Hukumar Askira/Uba ta jihar Borno.
Mazauna yankunan sun ce an kai farmakin kauyen ne da misalin 6:30 na yammacin ranar Talata kuma sun shafe kimanin sa’o’i biyu suna ta’asa.
A zantawarsu da Aminiya, mazauna yankunan sun nuna takaicinsu kan irin ta’adin da ’yan Boko Haram suka yi a harin.
Wasu daga cikin gine-ginen da suka kona bayan sace kayan ciki sun hada da shagunan kasuwanni, gidaje da kuma wuraren ibada.
Aminiya ta gano cewa daruruwan mazauna yankunan ne suka fantsama cikin dazuka domin tsira da rayuwarsu saboda irin harbin kan mai uwa da wabin da maharan suka rika yi a kauyen.
Wani mafarauci kuma mazaunin yankin, Steve Mamza ya ce sai washegari ranar Laraba ne suka dawo kauyen domin ganewa idanunsu irin ta’asar da aka yi.
A cewarsa, “Mun gode Allah cewa ba a samu asarar rayuka ba, amma dukiyoyinmu kuwa sun salwanta, ’yan Boko Haram sun kona gidajenmu sama da 30 a daren jiya [Talata].
“Sun lalata kusan dukkan muhimman abubuwa na garin.
“Ban san me ya sa koyaushe suke kawo mana hari ba; dukkan amfanin gonarmu sun lalata. Wannan abun takaici ne matuka,” inji Steve.
Sai dai wata majiya daga jami’an tsaro ta yi ikirarin cewa an kashe wasu daga cikin mayakan a kauyen Chul a kan hanyarsu ta guduwa bayan harin na Wamdeo.
Majiyar ta kara da cewa sojojin sun yi amfani da jirage yaki wajen yi wa ’yan ta’addan ruwan wuta a daren na Laraba.