Wasu da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kauyen Sassawa da ke karamar hukumar Damaturu da ke jihar Yobe inda suka kashe sojoji takwas.
Wani babban jami’in tsaro ya fada wa Aminiya cewa maharan sun kai hari kauyen ne a jerin motocin A-kori-kura biyar da misalin karfe shida na yamma a ranar Talata inda suka budewa sojoji wuta.
“Maharan sun mamayi sojojin ne ta wani filin kwallon kafa. Wani babban jami’in soja da wasu bakwai sun mutu. Da dama kuma sun ji rauni”. Inji shi