An kashe mutane tara tare da jikkata wasu huɗu a wani da mayakan Boko Haram suka kai yankin a Malam Fatori da ke Jihar Borno.
Gwamna Babagana Zulum, wanda baya kasar a halin yanzu, ya tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Sugun Mai Mele, domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa da kuma tantance halin da ake ciki.
Mai Mele ya jaddada aniyar Gwamna Zulum na jajircewa wajen tabbatar da tsaron Malam Fatori saboda muhimmancinsa.
Ya sanar da shirin tura manyan injina domin tona ramuka a kusa da hedikwatar ƙaramar hukumar don hana hare-hare nan gaba daga Boko Haram da ISWAP.
- Turji: Sai ka sako mutanen da ka sace za a yi sulhu — Gwamnatin Sakkwato
- Sarkin Ibadan ya rasu yayin da ake shirin bikin cikarsa shekara guda a mulki
Haka nan kuma ya gargaɗi mazauna yankin kan haɗin gwiwa da ’yan tawaye, inda ya yi barazanar “sakamakon Ubangiji” ga duk masu haɗin gwiwa.
An bayar da tallafin kuɗi, inda aka bai wa duk gidan da suka asa yan uwa ₦500,000, yayin da waɗanda suka jikkata huɗu kowannensu ya samu ₦250,000.
A halin yanzu, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Tsaro na Cikin Gida, Usman Tar, ya sanar da shirin sake tsugunar da ƙarin iyalai 3,000 da suka rasa matsugunansu a Malam Fatori, wanda hakan zai kai ga jimlar gidaje 5,000 da aka sake tsugunar da su.
Tar ya tabbatar wa mazauna yankin ci gaba da ƙoƙarin gwamnati na samar da matakan tsaro da kayan aiki don dawwamammen dawowar su, yana mai kira gare su da su ci gaba da kasancewa a faɗake tare da kai rahoton duk wani abu da ba a aminta da shi ba.