✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Boko Haram sun kashe kwamandojin ISWAP 2 da karin mayaka 32

Fada dai na ci gaba da kazancewa tsakanin bangarorin biyu a dajin na sambisa

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wani harin kwanton-bauna kan ’yan kungiyar ISWAP, inda suka halaka musu wasu manyan kwamandojin biyu da karin mayaka 32 a dajin Sambisa.

Kwamandojin da aka kashe wa ISWAP sun hada da Abu-Ikilima da Habu West.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa wani kwararre a kan harkar ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ta ce an yi arangamar ce a kauyukan Yale da ke Damboa da kuma Gargash da ke kusa da Nguro Soye a karamar hukumar Bama ta Jihar Borno.

Kungiyoyin biyu dai da ba sa ga-maciji da juna sun yi taho-mu-gamar ne lokacin da mayakan ISWAP ke tafiya da daddare kan hanyarsu ta zuwa wani sabon sansaninsu da aka kafa a kusa da kurwar Alafa a ranar 19 ga Afrilun 2022.

Majiyar ta kara da cewa, an kuma kama wasu mayakan na ISWAP guda hudu da ransu, sannan ’yan kungiyar sun yi nasarar kwace makamai tare da yi musu yankan rago.

Sun kuma samu nasarar kwace musu motocin daukar kaya guda uku.

Haka ila yau majiyar ta kara da cewa, a ranar 20 ga Afrilu, 2022, wani babban jigo a kungiyar ta Boko Haram, Ambu Mairamiri, wanda aka fi sani da Amir Fiyer ko Abou Ali, ya jagoranci dimbin mayakan Boko Haram dauke da muggan makamai suka kai farmaki a wani sansanin ISWAP da ke kusa da Nguro Soye, wanda ya kai ga kazamin fada wanda ya dauki sama da sa’a biyu ana gwabzawa a tsakaninsu.

Majiyoyin sun ce fadan ya yi sanadiyyar mutuwar mayakan ISWAP kusan 18, yayin da mayakan Boko Haram shida suka mutu a daya bangaren.

Mairamiri wanda ya sha alwashin kawar da dukkan ’yan ta’addan ISWAP a doron kasa, ya umarci mutanensa da su kona manyan motocin ISWAP guda hudu da kuma sabbin tantunan da suka kafa.

Sabon salon da rikicin bangarorin ’yan ta’addan biyu ya dauka a dajin na Sambisa ya sa ’yan Boko Haram na farautar ’yan ISWAP cikin dare saboda sanin yanayin da suke ciki, yayin da ISWAP ke hada kai don  kai harin ramuwar gayya da rana.

Haka nan wasu majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun ce hare-haren da sojoji suka kai a karkashin rundunar tsaro ta Operation Desert da kuma Operation Sanity,  sun tilasta wa ’yan ta’addar ISWAP da dama yin kaura zuwa wasu wurare mafi aminci.

Wuraren da suke komawa dai sun haɗa da kewayen tsaunin Mandara, Gargash, Izza, Bula Bakakai, Gobara da kuma dutsen Ngulde rock da ke kusa da garin Chibok.