Rahotanni na bayyana cewa, ‘yan Boko Haram sun baiwa jama’ar garin Jakana da Mainok da ke jihar Borno wa’adin barin garin ko kuma su kashe su.
A wata majiya daga garin Jakana na cewa ‘yan kungiyar sun baiwa jama’ar garin wa’adin yau Laraba su fice daga garin ko kuma su fuskanci hari.
Wani mazaunin garin ya bayyana wa manema labarai cewa, bayan kai harin Aunu ‘yan Boko Haram sun aiko mana da wasiqar barin garin yau.