✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Boko Haram na tilasta aurar da kananan yara a Neja

“Sun tara mazauna yankin, suka basu umarnin aurar da duk yarinyar da ta kai shekara 12."

’Yan kungiyar Boko Haram sun fara tilasta wa mazauna Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja aurar da duk ’ya’yansu mata da suka kai shekara 12.

Mazauna yankin sun ce ’yan ta’addan sun kuma bukace su da kada su yi biyayya ga kowacce irin hukuma ta gwamnati.

Wani mazaunin yankin, kuma jagoran Kungiyar Masu Kishin Shiroro, Bello Ibrahim, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Akwai lokacin da suka je Kawure, kauyen tsohon Sanata mai waliktar Neja ta Gabas, David Umaru.

“Amma sojoji sun yi nasarar fatattakarsu. Sai dai sakamakon babu sansanin sojoji a yankin, sun sake dawowa.

“Yanzu haka, suna nan a kauyen na Kawure, kuma sun fara bazuwa zuwa wasu yankunan Kuregbe da Awulo, da wasu yankunan.

“A Awulo da Kuregbe, sun tara mazauna yankin, Musulmi da Kirista sannan suka basu umarnin cewa duk yarinyar da ta kai shekara 12 dole a aurar da ita.

“Babu wata doka da ake amfani da ita a yankin, in ban da ta Boko Haram. Idan mutane suka sami rashin jituwa, ko tsakanin dangi ko ta zamantakewa, gurinsu ake zuwa su yi sulhu.

“Ba wanda ya isa ya kai kara wajen ’yan sanda ko kotu ko kowacce irin hukuma,” inji Bello Ibrahim.

Wani mazaunin yankin shi ma ya ce ’yan kungiyar na ta kai da kawonsu a yankin ba tare da wani tarnaki ba.

“Sun zama sune hukuma a kauyukan. Da Kawure da Awulo da Kuregbe nan ne ya zama sansaninsu, kuma mabiya yankunan dole suke yi musu biyayya.

“A gundumomin Chukuba da Kuregbe, ’yan Boko Haram ne suke cin karensu ba babbaka, ba ma ’yan bindigar da muka sani ba.”

Shugaban Karamar Hukumar ta Shiroro, Suleiman Chukuba ya tabbatar da kwararowar ’yan kungiyar a yankinsa, inda ya ce, “A kan batun kwararowarsu a Shiroro, gundumomi hudu ne lamarin ya shafa.

“Yanayin irin wa’azin da suke yi ne ya sa mutane suka fahimci cewa ’yan Boko Haram din ne.

“Sun shaida wa mazauna kauyukan cewa za su basu kudi da bindigogi domin su yaki gwamnati, wannan kowa ya san ita ce akidar ’yan Boko Haram,” inji shi.

Sai dai mazauna yankin sun ce ya zuwa yanzu babu wanda suka fara tilasta wa ya shiga kungiyar, in ban da hana su kai kara wajen ’yan sanda da kotuna da suke yi da kuma batun aurar da matan.