✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Boko Haram 190 sun sake mika wuya a Borno

Mayakan sun nemi 'yan Najeriya da su yafe musu.

Mayakan Boko Haram 190 tare da iyalansu sun mika wuya ga sojojin Najeriya a Karamar Hukumar Mafa da ke Jihar Borno a cewar wata majiyar jami’an tsaro.

Aminiya ta ruwaito cewa mazauna garin sun yi mamakin lokacin da suka ga dimbin ‘yan ta’addan da suka isa garin Mafa a ranar Asabar.

  1. Cewa masu garkuwa da ni na yi sam ban san matata ba – Kwamishinan Neja
  2. Kotu ta daure masu kwacen waya shekara 7 a kurkuku

A cewar jami’an tsaro, majiyar ta ce wadanda suka mika wuya sun hada da manyan mayakan Boko Haram, matansu da yaransu.

‘Yan ta’addan da suka mika wuya sun kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su gafarta musu tare da tabbatar wa mazauna yankin cewa sun mika wuya bisa ga ra’ayinsu na kashin kai.

Ana iya tuna cewa, mahukunta a Najeriya sun yi ikirarin cewa jimillar ‘yan ta’adda 1081 da iyalansu sun mika wuya ga sojoji cikin makonni biyu da suka gabata.

A makon da ya gabata wasu daga cikin mayakan Boko Haram da suka ajiye makamai sun kuma nemi afuwar ‘yan Najeriya game da irin barnar da suka tafka a baya.

Hakan ya janyo zazzafar muhawara a tsakanin ‘yan Najeriya, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa game da lamarin.

Wasu na ganin cewar sun cancanci a yafe musu matukar sun yi tuba na hakika inda kuma wasu ke da sabanin wannan ra’ayi.