✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bingida sun yi garkuwa da Rabaran a Abuja

Masu garkuw da mutane sun sace wani Rabaran a yankin Yangoji da ke Birnin Tarayya, Abuja.

Wasu ’yan bingida da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Rabaran Matthew Dajo, na Cocin Katolika ta St. Anthony a kauyen Yangoji a Abuja.

Wani mazaunin yankin mai suna Saleh, ya ce ’yan bingidar sun shiga gidan Rabaran din ne da misalin karfe 9:47 na dare a ranar Lahadi, suka tafi da shi.

“A zahiri mutane sun firgita sakamakon harbin bindiga da suka rika yi.

“Babu wanda ya samu damar fitowa kuma wasu daga cikinsu sun kewaye gidan, wasu kuma suka haura katangar gidan”, inji Saleh.

A cewarsa, ’yan bindigar sun yi ta harbi sama da nufin razana mutane, daga bisani suka yi awon gaba shi zuwa cikin daji.

Lokacin da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf, ta tabbatar da yin garkuwa da limamin cocin.

A cikin wani jawabi, jami’ar ta ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Birnin Tarayya Bala Ciroma, ya kafa tawagar da za su bi sahun masu garkuwar don cafke su.