A yayin da sha’anin tsaro ya tabarbare a yanzu, ‘yan bindiga na iya sace Shugaba Muhammadu Buhari a cewar Buba Galadima, wani tsohon na hannun daman Shugaban kasar.
Buba Galadima ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC kan ya yadda matsalar tsaro ta tabarbare a kasar nan.
- LABARAN AMINIYA: Yajin Aikin ASUU: Yadda Muke Rayuwa Ba Tare Da Albashi Ba — Malaman Jami’a
- ’Yan bindiga sun sake sace matar Sarkin Fulani a Abuja
Tsohon dan siyasar ya bayyana cewa, a halin da ake ci a yanzu, ba zai yi mamaki ba idan ‘yan bindigar da suka yi barazanar sace shugaban kasar suka aikata hakan.
A cewar Buba Galadima, “‘Yan bindigar nan sun raina gwamnatin Buhari.
“A farkon mulkinsa kowa na tsoronsa, ana yi masa zaton jarumta da karfin fada a ji, amma yanzu ta bayyana cewa ba zai iya komai ba.
“Buhari bai san komai ba, ba kuma zai iya komai ba.
“Wannan dalili ya sa ake samun rahotannin jami’an gwamnati na satar biliyoyi na dukiyar al’umma babu wanda ya isa ya hana su.”
Galadima ya kara da cewa, idan har ‘yan ta’adda za su iya fasa gidan yari na Kuje, toh, lallai Buhari ma ba zai tsira ba.
“Muddin ba a dauki matakan da suka dace ba, kuma aka ci gaba da tafiya a irin wannan yanayi, za a kai lokacin da Buharin ma za a iya sace shi, ganin yadda ake wasarairai da sha’anin tsaro.
“Mafita garemu ita ce a yanzu shi ne ko mu ci gaba da addua’a, ko kuma mu tanadi makaman da za mu kare kanmu.
“Amma idan muka dogara da wannan gwamnati, tabbas halakamu za a yi.”
Ita ma Hajiya Naja’atu Mohammed, wata babbar ‘yar siyasa, kuma tsohuwar ta hannun dama ga shugaba Buhari, ta yi makamanciyar wannan magana a hirarta da DW farkon makon nan.